An jefi motar Manchester United a Liverpool

Kungiyar Liverpool ta ce bai kamata da aka jefi motar Manchester United ba, kafin su kara ranar Lahadi a Anfield.

Liverpool da Manchester United sun tashi 0-0 a wasan mako na 17 a Premier League ranar Lahadi.

Mahukuntan Liverpool sun ce za su hada kai da ‘yan sanda domin zakulo wadanda suka aikata laifin, domin su fuskanci hukunci.

Lokacin da motar Man United ta kusan kai wa kata faren filin Anfield ne, sai wasu suka yi ta jifan motar da abubuwa da yawa.

Wani bidiyo a kafar sada zumunta ya nuna inda gilashin tagar motar ya fashe, wanda kamar da kwalba aka yi jifan.

Da wannan sakamakon Liverpool ta koma ta biyun teburi da tazarar maki daya tsakaninta da Arsenal.

Ranar ta Lahadi, Arsenal ta doke Brighton 2-0 a Emirates, hakan ya sa ta koma matakin da take a baya can.

Leave a comment