Ten Hag bai damu da batun korar shi daga Man United ba

Kociyan, Manchester United, Erik ten Hag ya ce ya mayar da hankali kan yadda kungiyar za ta koma kan ganiya, bayan da ake cewa ana daf da korar shi.

Man United za ta kara da Liverpool ranar Lahadi a gasar Premier League, daya daga wasa mai zafi da za ta fuskanta.

Tun kan nan Man United ta yi rashin nasara a hannun Bournemouth da ci 3-0 a Old Trafford ranar Asabar a Premier League, sannan aka fitar da ita a Champions League.

Man United ta kare a matakin karshe a teburin zakarun Turai da maki hudu, an fitar da ita a League Cup, tana ta shidan teburin Premier League.

Mai rike da kofin Premier League 20, ta yi rashin nasara 12 a dukkan fafatawa a bana, ana cewa Sir Jim Ratcliff zai dauki Graham Potter, idan ya kammala sayen hannun jarin kungiyar mafi rinjaye.

Liverpool tana ta daya a teburin Premier League, wadda ba a doke ta ba tun cikin Satumba a gasar, amma Ten Hag ya ce zai tayar da hankalin kungiyar Anfield.

Man United za ta buga wasan ba tare da Harry Maguire ba, wanda ya ji rauni a wasa da Bayern Munich a Old Trafford.

Haka shima Luke Shaw ba zai samu buga wasan na hamayya ba, sakamakon jinya, wanda ya ji rauni a gasar ta Champions League da kungiyar Jamus.

Leave a comment