Osimhen zai ci gaba da wasa a Napoli

Wasu rahotanni na cewa dan kwallon tawagar Nigeria, Victor Osimhen ya amince da kwantiragin ci gaba da taka leda a Napoli.

Dan wasan ya koma buga a Serie A daga Lille a 2020, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar badi a Italy.

Rawar da Osimhen ya taka a kakar da ta wuce ana alakanta mai shekara 24 da zai koma Arsenal ko Chelsea ko kuma Manchester United.

Sabuwar yarjejeniyar Osimhen za ta kare a karshen kakar 2026, za kuma a biya Napoli €130m idan kungiya za ta dauki dan wasan kwantiraginsa bai cika ba da za ta fara aiki daga 2024.

Osimhen yana gaba-gaba da manyan kungiyoyi ke son dauka da zarar an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a kaka mai zuwa, wanda ya ci kwallo 26 a wasa 32 a bara.

Hakan ya sa Napoli ta lashe Serie A karon farko a tarihi tun bayan shekara 33 lokacin Diego Maradona.

Ya lashe kyautar fitatcen dan kwallon Serie A da kuma gwarzon dan wasan Afirka yak are a mataki na takwas a takarar Ballon d’Or.

A kakar da ake buga wa ta bana, Osimhen ya ci kwallo bakwai a wasa 15 a Napoli.

Dan wasan Nigeria ya ci kwallo 66 ya bayar da 16 aka zura a raga a wasa 116 da ya yiwa Napoli, wadda ta sayo shi daga Lille kan €75m.

Leave a comment