Ko PSG za ta iya cin Borussia Dortmund?

Borussia Dortmund ta karbi bakuncin Paris St Germain, domin buga wasan karshe a cikin rukuni a Champions League ranar Laraba.

Dortmund ce ta daya a rukuni na shida da maki 10, sai kungiyar Faransa mai maki bakwai, bayan wasa biyar a rukuni.

Newcastle United da AC Milan kowacce tana da maki biyar, wadanda za su fafata a St James Park a daya wasan cikin rukunin.

A wasan farko da suka kara cikin Satumba, Paris St Germain ce ta ci 2-0, daya wasan kuwa tashi aka yi 0-0 tsakanin Milan da Newcastle United.

Shin ko kun san?

Niclas Füllkrug, wanda ya fara buga Champions League a bana a karawar France ya ci kwallo shida ya bayar da hudu aka zura a raga a dukkan fafatawa.

Julian Brandt na Dortmund ya ci kwallo shida a Champions League a 2023/24.

Marco Reus shi ne dan wasan Dortmund mai kwallo 23 da ya zura a raga a Champions League jimilla.

Kwallo uku ne ya shiga ragar Borussia Dortmund – iri daya da aka zura a ragar Arsenal da Barcelona – Real Sociedad ce kadai aka zurawa kwallo biyu kacal a bana a gasar.

PSG ta yi rashin nasara 2-1 a Dortmund a 2019/20 zangon zagaye na biyu. Daya daga rashin nasara shida da ta yi a wasa 13 a Jamus a gasar zakarun Turai.

Dan wasan da PSG ta dauka a bana, Randal Kolo Muani ya ci kwallo 26 a Bundesliga lokacin da yake Eintracht Frankfurt a bara.

Leave a comment