Germany za ta kara da France da Netherlands a Maris

Tawagar Jamus za ta buga wasan sada zumunta da France da Netherlands a cikin watan Maris din 2024.

Germany za ta yi wasannin ne, domin gwada ‘yan wasan da za ta yi amfani da su a Euro 2024.

Kasar ce za ta karbi bakuncin wasannin gasar cin kofin nahiyar Taurai da za a yi a cikin Yuni zuwa Yulin 2024.

Germany za ta fara wasan sada zumunta da Franceranar 23 ga watan Maris a Lyon, kwana uku tsakani ta karbi bakuncin Netherlands a Frankfurt.

Germany ta ci France 2-1 cikin watan Satumba karkashin Rudi Voller, bayan da ta kori, Hansi Flick.

Germany, wadda ke fuskantar koma baya na fatan komawa kan ganiya karkashin Julian Nagelsmann.

Tsohon kociyan Bayern Munich ya fara cin Amurka 3-1 da yin 2-2 da Mexico daga baya Turkey ta doke su 3-2 da rashin nasara 2-0 a hannun Austria.

Germany za ta fara gasar Euro 2024 ranar 14 ga watan Yuni, inda za ta kara da Scotland, sai ta fuskanci Hungary ranar 19 a watan Yuli ta karkare da Switzerland ranar 23 ga watan Yuni.

Italy ce mai rike da kofin wadda ta doke England a Wembley ta lashe kofin na Euro 2020.

Leave a comment