Ibrahimovic ya koma AC Milan a matakin mai bayar da shawara

Zlatan Ibrahimovic ya sake komawa AC Milan amma a matakin mai bayar da shawara ga masu kungiyar, RedBird Capital Partners.

Cikin aikin da mai shekara 42 zai yi, sun hada da samo sabbin masu zuba jari da tallata kungiyar da kula da harkokin yanar gizo da yadda za a kara bunkasa Milan.

Ibrahimovic ya taka rawar gani da kungiyar ta koma kan ganiya tun bayan da ya koma Milan a 2019.

Hakan ya sa AC Milan ta lashe kofin Serie A a 2022 tun bayan shekara 11, bayan da abubuwa suka yi mata kasa a fannin tamaula a baya.

A sana’ar tamaula da Ibrahimovic ya yi ya lashe kofi a Netherlands da Italy da Spain da France, koda yake babban kofi da ya dauka a Turai shi ne Europa League a Manchester United a 2017.

Leave a comment