‘Yan Real Madrid da za su kara da Union Berlin

Real Madrid ta ziyarci Union Berlin, domin buga wasa na shida a rukuni na uku a Champions League ranar Talata.

Tuni Real Madrid mai Champions League 14 ta kai zagayen gaba da maki 15, ita kuwa Berlin maki biyu ne da ita.

Haka kuma a dai rukuni na uku a daren nan za a fafata tsakanin Napoli da Sporting Braga.

Ranar 20 ga watan Satumba, Real Madrid ta ci Union Berling 1-0 a Spain, yayin da Napoli ta je ta doke Braga 2-1 a daya karawar rukuni na uku.

Napoli tana da maki bakwai, yayin da Sporting Braga keda maki hudu, za a kammala wasannin karshen rukuni ranar Talata.

Wannan shi ne wasa na biyu da Real Madrid za ta fafata da Union Berling a gasar ta zakarun Turai.

‘Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Lunin, Kepa, Fran.

Masu tsaron baya: Alaba, Nacho, Lucas V., Fran García, Rüdiger, Mendy, Tobias.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Valverde, Ceballos, Mario Martín, Nico Paz.

Masu cin kwallaye: Rodrygo, Joselu, Brahim, Gonzalo.

Wasannin da za a buga ranar Talata:

  • PSV Eindhoven da Arsenal     
  • Lens da Sevilla
  • Manchester United da Bayern Munich  
  • Inter Milan da Real Sociedad 
  • FC Union Berlin da Real Madrid
  • Napoli da Sporting Braga        
  • Red Bull Salzburg da Benfica  
  • FC Kobenhavn da Galatasaray

Leave a comment