Ko mANCHESTER UNITED ZA TA CI BAYERN MUNICH KUWA?

Manchester United za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasan karshe a rukunin farko a Champions League ranar Talata.

Bayern Munich ta kai zagayen gaba da maki 13, bayan wasa biyar a cikin rukuni, ita kuwa United tana ta karshen teburi da maki hudu.

Daya wasan rukunin farko shi ne tsakanin FC Copenhagen da Galatasaray, wadanda kowacce take da maki biyar.

United na bukatar doke Bayern Munich a Old Trafford, sannan ta yi fatan a tashi canjaras a daya wasan.

Ranar 20 ga watan Satumba a wasan farko a cikin rukuni, Bayern ta ci United 4-3 a Jamus a ranar aka tashi 2-2 tsakanin Galatasaray da FC Copenhagen.

Wannan shi ne wasa na 13 da za a kara tsakanin kungiyoyin, inda Bayern ta ci wasa biyar da canjaras biyar, United ta yi nasara biyu.

Wasannin da za a buga ranar Talata:

  • PSV Eindhoven da Arsenal     
  • Lens da Sevilla
  • Manchester United da Bayern Munich  
  • Inter Milan da Real Sociedad 
  • FC Union Berlin da Real Madrid
  • Napoli da Sporting Braga        
  • Red Bull Salzburg da Benfica  
  • FC Kobenhavn da Galatasaray

Leave a comment