Za a gama wasan rukuni a Champions League Talata da Laraba

Ranar Talata da Laraba za a kammala wasannin cikin rukuni a gasar Champions League ta bana.

Za kuma a buga wasa takwas ranar Talata a kammala da wasu takwas ranar Laraba.

Za kuma a yi tata burza tsakanin rukunin farko zuwa na hudu, inda kowanne rukuni zai yi wasa tare a ranar.

Ranar Talata rukunin farko zai yi wasa, inda za a kara tsakanin Manchester United   da Bayern Munich da na FC Copenhagen da Galatasaray.        

Kungiyar Jamus ce ta daya da maki 13 ta kai zagayen gaba, sai Copenhagen da Galatasaray masu maki biyar-biyar.

Manchester United ce ta hudun teburi da maki hudu, wadda ke fatan cin Bayern Munich, mai fatan daya wasan a tashi canjaras

Rukuni na biyu kuwa za a kece raini tsakanin PSV Eindhoven da Arsenal da na Lens da Sevilla.

Gunners ta kai zagaye na biyu a gasar mai maki 12, ranar Talata za a fayyce ta biyu da za ta bi sawun Arsenal.

PSV Eindhoven maki takwas ne da ita da kuma Lens mai biyar, yayin da aka yi waje da Sevilla mai maki biyu.

Real Madrid ma ta kai zagayen gaba a rukuni na uku da maki 15, bayan da ta lashe dukkan fafatawa biyar da ta yi a rukunin.

Real Madrid za ta je gidan Union Berlin a Jamus ranar Talata, yayin da Napoli za ta karbi bakuncin Sporting Braga.

Napoli ce ta biyu mai maki bakwai, sai Sporting Braga mai hudu da kuma Union Berlin mai biyu.

Rukuni na hudu da zai yi wasa ranar Talata ya hada da fafatawa tsakanin Inter Milan da Real Sociedad da na Red Bull Salzburg da Benfica.

Real Sociedad da Inter Milan sun kai zagayen gaba, bayan da kowacce take da maki 11, yanzu dai so ake a fayyace ta daya da ta biyu.

Red Bull Salzburg maki hudu ne da ita da kuma Benfica mai daya.

Wasannin da za a buga ranar Talata:

  • PSV Eindhoven da Arsenal     
  • Lens da Sevilla
  • Manchester United da FC Bayern Munich        
  • Inter Milan da Real Sociedad 
  • FC Union Berlin da Real Madrid
  • Napoli da Sporting Braga        
  • Red Bull Salzburg da Benfica  
  • FC Kobenhavn da Galatasaray

Leave a comment