Lacazette ya ci kwallo uku da Lyon ta doke Toulouse

Alexandre Lacazette ya yi sanadin da Lyon ta yi nasara a wasa na biyu a Ligue 1 a bana, bayan da ta ci Toulouse 3-0 ranar Lahadi.

Kyaftin din Lyon, Lacazette shi ne ya ci kwallo uku a karawar a wasan da suka ci kungiyar da take ta 15 a gasar ta Faransa.

Nasarar da Lyon ta samu ya kara karfin gwiwar kungiyar da ke karshen teburi mai maki 10 a fafatawa 15.

Karon farko da kungiyar ta samu nasara tun bayan korar koci, Fabio Grosso sakamakon da ba ta kokari a bana.

Paris St Germain ce ta daya a Ligue 1 da maki 35, sai Nice mai maki 32 da Monaco ta uku da maki 30, bayan karawa 15.

Kylian Mbappe na PSG ne kan gaba a yawan cin kwallaye mai 15 a raga, Akor Adams na Montpellier mai bakwai a raga.

Sauran da ke da shida-shida sun hada da Alexandre Lacazette na Lyon da Mostafa Mohamed na Nantes da kuma Wissam Ben Yedder da ke Monaco.   

Leave a comment