Ake ya buga wa Manchester City wasa na 100

Nathan Ake ya buga wa Manchester City wasa na 100 a karawar da ta doke Luton Town 2-1 a Premier League ranar Lahadi.

Kenan ya zama na 22 da ya buga wasa 100 karkashin Pep Guradiola, kuma na farko daga Netherlands.

Cikin wadanda suka yi fafatawa sama da 100 a Man City sun hada da Bernardo Silva (324), Kevin De Bruyne (317), Ederson (309), Kyle Walker (276), Phil Foden (240), John Stones (237), Rodrigo (226), Ruben Dias (153) da kuma Jack Grealish (105).

Cikin wasa 100 da Ake ya buga, an fara 75 da shi a cikin fili, an kuma ci karawa 68 da canjaras 16 da rashin nasara 16 tare da shi.

Wanda ya ci kwallo tara a kungiyar Etihad, ya buga wasa 23 da ta yi ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba.

Man City tana mataki na hudu a teburin Premier League da maki 33, bayan wasa 16 a bana.

Liverpool ce ta daya da maki 37, sai Arsenal mai 36 da kuma Aston Villa ta uku mai maki 35.

Leave a comment