Gnabry ba zai buga wa Bayern Munich wasa da Man United ba

Dan wasan Bayern Munich, Serge Gnabry ba zai buga karawar da kungiyar Jamus za ta yi da Manchester United ba ranar Talata.

Manchester United za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasa na karshe a rukunin farko a Champions League a Old Trafford.

Tuni dai Bayern Munich ta kai zagayen gaba a gasar ta zakarun Turai, ita kuwa Man United tana ta hudun teburi da maki hudu kacal.

FC Copenhagen da Galatasaray da za su kara a dai ranar Talata a rukunin farko kowacce tana da maki biyar-biyar.

Idan har Man United za ta kai zagaye na biyu a Champions League sai ta ci Bayern Munich, sannan daya wasan su tashi canjaras.

Gnabry ba zai je wasan da za a buga a Old Trafford ba, sakamakon raunin da ya ji a karawar da Eintracht Frankfurt ta caskara Bayern Munich 5-1 a Bundesliga ranar Lahadi.

Haka kuma kociyan Bayern Munich, Thomas Tuchel zai buga wasan ba tare da Matthijs de Ligt da Bouna Sarr da Tarek Buchmann da kuma Gabriel Marusic, wadanda ke jinya.

Leave a comment