Girona ta ci Barcelona ta koma ta daya a La Liga

Barcelona ta yi rashin nasara a gida a hannun Girona da ci 4-2 a gasar La Liga ranar Lahadi.

Kungiyar da Michel ke jan ragama ta yi nasara a kan Barca, abokiyar hamayya a karon farko a tarihin gasar.

Barcelona da Girona sun buga wasa na bakwai a La Liga, inda kungiyar da Xavi ke horarwa ta ci hudu da canjaras biyu.

Sun fara haduwa a La Liga ranar 23 ga watan Satumbar 2017, inda Barcelona ta ci 3-0 a gidan Girona.

A wasa na biyu Girona ta yi rashin nasara 6-1 a gidan Barcelona ranar 24 ga watan Fabrairun 2018.

Nasarar da Girona ta samu ya sa ta koma ta daya a teburin La Liga da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid ta biyu.

Ranar Asabar Real Madrid ta je ta tashi 1-1 a gidan Real Betis, inda Jude Bellingham ne ya ci mata kwallo na 12 a gasar.

Ita kuwa Barcelona mai rike da kofin bara ta yi kasa zuwa mataki na hudu, sakamakon da Atletico Madrid, wadda ta koma ta uku da yi nasara a kan Almeria.

Girona ta bai wa Barcelona tazarar maki bakwai.

Leave a comment