Frankfurt ta cascara Bayern Munich 5-1

Eintracht Frankfurt ta casa Bayern Munich da ci 5-1 a wasan mako na 14 a Bundesliga ranar Asabar.

Frankfurt ta ci kwallayen ta hannun Omar Marmoush da Eric Ebimbe da Hugo Larsson da Eric Ebimbe da kuma Ansgar Knauff.

Bayern Munich ta zare daya ta hannun Joshua Kimmich daf da za su je hutun rabin lokaci.

Bayern Munich ta sa ran cin wasan, domin ta dare matakin farko a ranar Asabar, kafin ta ga abinda zai faru Lahadi.

Karo na biyu da Frankfurt ta dura 5-1 a Bayern Munich kamar yadda ta fara a 2019, hakan ta sa aka kori koci, Niko Kovac.

Da wannan sakamakon Bayern ta ci gaba da zama ta biyu a teburi da tazarar maki uku tsakaninta da Bayer Leverkusen ta daya, wadda za ta kara da Stuttgart ta ukun teburi ranar Lahadi.

Ita kuwa Union Berlin ta fito daga gurbin ‘yan karshen teburi ta koma ta 15, bayan doke Borussia Munchengladbach 3-1.

Freiburg ta ci 1-0 a gidan Wolfsburg, Werder Bremen ta doke Augsburg 2-0, Heidenheim ta yi nasara a kan Darmstadt 3-2

Leave a comment