Salah ya ci kwallo na 200 a Liverpool

Crystal Palace ta yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Liverpool a wasan mako na 16 a Premier League.

Jean-Philippe ne ya fara ciwa Palace kwallo daga baya Mohammed Salah ya farkewa Liverpool kwallon.

Daf da lokaci zai cika ne Liverpool ta ci na biyu ta hannun Harvey Elliott da ya sa ta hada maki uku a karawar.

Palace ta karasa wasan da ‘yan kwallo 10 a cikin filin, bayan da aka bai wa Jordan Ayew jan kati.

Kwallon da Salah ya ci shi ne na 200 a dukkan karawa a kungiyar, ya zama na biyar a Liverpool mai wannan kwazon.

‘Yan wasan Liverpool ne suka ci kwallo karo uku daga hudu da ake ci a minti 90 din karshe.

Jota ya yi hakan a wasan da Tottenham a Afirilun da wadda Nunez ya yi a cikin watan Agusta da kuma Elliott a wasan Palace.

Leave a comment