Kyrgios ya janye daga Australian Open

Tsohon wanda ya buga wasan karshe a Wimbledon Open, Nick Kyrgios ya janye daga shiga Australian Open karo na biyu kenan a jere.

Wasa daya kacal mai shekara 28 ya buga a kakar 2023 a Stuttgart cikin watan Yuni.

Kyrgios ya hakura shiga gasar a daf da yake shirin buga wasannin zagayen farko a Melbourne Park a Janairun 2024, tun can baya ya sanar za a yi masa aiki a gwiwarsa.

Tun farko ya dauka yar karamar jinya zaiyi, amma sai cikin watan Yuni ya koma wasa, nan ma bai murmure ba kamar yadda ya kamata.

Kyrgios, wanda ya kai wasan karshe a Wimbledon a 2022, ya janye daga buga wasannin 2024, wannan karon ya yi korafin ciwon tsntsiyar hannu, an kuma daina ganin shi a wajen atisaye.

Kyrgios, wanda baya jadawalin jerin ‘yan wasan da ke taka rawar gani a kwallon tennis sakamakon doguwar jinya, ya ce zai je Melbourne zai bayar da gudunmuwa.

Leave a comment