Man United ta koma ta shidan teburin Premier

Manchester United ta doke Chelsea 2-1 a wasan mako na 15 a gasar Premier League ranar Laraba a Old Trafford.

United ta ci kwallayen ta hannun Scott McTominay, yayin da Chelsea ta zare daya ta hannun Cole Palmer.

Hakan zai dan rage matsi a kan Erik ten Hag da yake fuskanta, yanzu ya koma kan Mauricio Pochettino.

United ta taka rawar da ba ta taba yi ba a bana, wasu na cewar martani ta mayar, bayan rashin nasara 1-0 a gidan Newcastle United ranar Asabar.

Wasa na shida da United ta yi nasara daga takwas, hakan ya sa ta koma ta shidan teburi da tazarar maki uku tsakaninta da Manchester City ta hudu.

Chelsea wadda ta kasha £1 billion ($1.26 billion) wajen sayo sabbin ‘yan wasa tana ta 10 teburin Premier League.

Leave a comment