An yi wa Wozniacki alfarmar shiga Australia Open

Ranar Laraba an bai wa Caroline Wozniacki gurbin shiga wasan gasar Australian Open ta 2024.

Karon farko da za ta koma buga wasannin a Melbourne tun bayan shekara hudu, wadda ta taba lashe kofin a 2018.

Mai shekara 33 ta yi ritaya, bayan Australian Open a 2020, amma ta sake komawa wasan a gasar Montreal a cikin watan Agusta.

Mai ‘ya ’ya biyu ta fara buga Grand Slam a karon farko a shekara uku a US Open, wadda ta kai zagayen quarter finals.

Za a fara Australian Open daga 14 zuwa 28 ga watan Janairu, yayin da Aryna Sabalenka da Novak Djokovic za su kare kofunansu..

Leave a comment