Bayern Munich ta dauki Bryan Zaragoza

Bayern Munich ta cimma yarjejeniyar daukar dan wasan Granada, mai shekara 22, Bryan Zaragoza.

Dan wasan zai koma kungiyar Bundesliga a kakar 2024/25, wanda zai saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar da za ta kare a karshen 2029.

Kamar yadda wasu rahotannin suka ce, Bayern Munich za ta biya €15 million ($16.18 million) kudin sayen dan kwalon.

Kenan za ta biya fiye da kudin da kungiyar ta gindaya wajen sayen matashin dan wasan kan €14 idan kwantiraginsa bai kare ba.

Tun farko RB Leipzig mai buga Bundeslida da mai buga Premier League, Brentford sun so daukar matashin.

Ana kwatanta Zaragoza da dan kwallo mai taka leda da zafi, wanda ya kware a zamiya a tsakanin ‘yan wasa.

Ya ci kwallo 10 ya bayar da uku aka zura a raga a wasa 51 da ya buga wa Granada.

Mai taka leda daga gefe ya fara buga wa tawagar Spain tamaula a cikin Oktoba a Euro 2024 da ta ci Scotland 2-0.

Leave a comment