Arsenal ta je ta doke Luton Town 4-3 a wasan mako na 15 a gasar Premier League.
Arsenal ta ci kwallayen ta hannun Gabriel Martinelli da Gabriel Jesus da Kai Havertz da kuma Declan Rice.
Ita kuwa mai masaukin baki Luton ta ci ukun ta hannun Gabriel Osho da Elijah Adebayo da kuma Ross Barkley.
A karawar Bukayo Saka ya buga wa Arsenal wasa na 200 a dukkan fafatawa.
Mai shekara 22 da kwana 91 ya zama dan Ingila na biyu da ya buga wa Gunners wasa da yawa, bayan Cliff Bastin a 1934.
Da wannan sakamakon Gunners ta hada maki 36 tana ta daya a teburin Premier, bayan wasa 15 da ta buga.
Sauran wasannin da za a buga ranar Laraba:
Fulham da Nottingham Forest
Crystal Palace da Bournemouth
Sheffield United da Liverpool
Brighton da Brentford
Aston Villa da Manchester City
Manchester United da Chelsea