An raba gari tsakanin Kluivert da Adana

Kungiyar Adana Demirspor da Patrick Kluivert sun raba gari, sakamakon kasa taka rawar gani a gasar Turkiya ta bana.

Wasa daga ta ci daga shida da ta buga a baya-bayan nan a lik din Turkiya.

Kungiyar ta sanar cewar ‘’Mun raba gari da Mr Patrick Kluivert,’’ wadda take ta biyar din teburi.

‘’Muna godiya ga Mr Kluivert da wadanda suka taimaka masa aiki da gudunmuwar da suka bai wa kungiyar, kuma muna musu fatan samun nasara a kan aikin su na gaba.’’

Kluivert mai shekara 47, bai dade da karbar aikin kocin ba kuma karon farko a babban mai horar da tamaula, bayan da ya bar Curacao zuwa Turkey.

Kluivert tsohon dan wasan Ajax da Barcelona, yana da mataimaka da suka hada da Mario Balotelli da Nani da M’Baye Niang da Younes Belhanda da kuma Benjamin Stambouli.

Haka kuma Demirspor ta fara kakar da kafar dama daga baya abubuwa suka lalace mata.

Amma doke ta 3-2 da wadda take kasan teburi, Samsunspor ta yi shi ne ya tada kura.

Leave a comment