Premier League ta sake salo a bana – Arteta

Mikel Arteta ya ce gasar Premier League ta sake salo daga wasannin da aka buga a bara.

Arsenal, wadda ke fatan bayarda tazarar maki biyar a teburi, za ta ziyarci Luton Town a wasan mako na 15 ranar Talata.

Gunners, wadda ta doke Wolverhampton 2-1 ranar Asabar ta bai wa Liverpool tazarar maki biyu da maki uku tsakani da Manchester City, wadanda za su yi wasa ranar Laraba.

A bara ne Arsenal ta rike teburin Premier League kwana 248 daga baya Man City ta karbe ta kuma lashe kofin.

Kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama ta kuma dauki Champions League da FA Cup a kakar da ta wuce.

Arteta ya kara da cewar gasar bana ta kara zafi fiye da bara a shirin da yake na lashe kofin a karon farko.

Rabonda Arsenal ta dauki Premier League tun bayan kakar 2004.

Kociyan ya kara da cewar ya kasa tantance ko Arsenal ta bara da ta bana, wacce ta fi kyau a wasannin da suke yi.

Leave a comment