Roma na daf da shiga ‘yan hudun farko a Serie A

Kungiyar Roma na daf da shiga cikin ‘yan hudun farko a gasar Serie A, bayan da ta doke Sassuola 2-1 ranar Lahadi.

Roma wadda take ta biyar a teburi, tana da maki 24, iri daya da na Napoli ta hudu.

Mai masukin baki ne suka fara cin kwallo ta hannun Matheus Henrique daga baya Roma ta farke ta hannun Paulo Dybala a bugun fenariti.

Roma ta zura na biyu a raga saura minti takwas a tashi wasan ta hannun Rasmus Kristensen.

Juventus ce ta daya a Serie A da maki 33, sai Inter Milan mai maki 32 da kuma AC Milan ta uku mai 29.

Leave a comment