Leverkusen ta kusan rasa matakinta a Bundesliga

Kadan ya rage Bayern Leverkusen ta rasa gurbinta na farko a Bundesliga, bayan da ta tashi 1-1 da Borussia Dortmund ranar Lahadi.

Borussia Dortmund ce ta fara cin kwallo a minti na biyar da take leda ta hannun Julian Ryerson.

Daga baya ne Leverkusen ta farke ta hannun Victor Boniface, saura minti 11 a tashi daga fafatawar.

Leverkusen ta samu damar bai wa Bayern Munich tazarar maki ,amma hakan bai yiwuba.

Ranar Asabar aka dage wasan da ya kamata Bayern Munich ta karbi bakuncin Union Berlin, sakamakon rashin kyawun yanayi.

Dortmund tana kan ganiya a bana, wadda ta doke Borussia Munchengladbach 4-2 a makon jiya a Bundesliga.

Sannan ta yi nasara a kan AC Milan 3-1 a Italy, wadda ta kai zagayen gaba a Champions League.

Ana kuma saka ta cikin ‘yan sawun gaba da ake cewar za ta iya lashe German Cup, wadda za ta ziyarci Stuttgart ranar Laraba.

Kawo yanzu Leverkusen ta ci wasa 11 da canjaras biyu daga wasa 13 a Bundesliga a bana.

Yanzu saura maki uku tsakanin Leverkusen ta daya a teburin Bundesliga mai maki 35 da Bayern Munich mai kwantan wasa mai maki 32.

Leave a comment