Liverpool za ta ziyarci Arsenal a FA Cup

Arsenal za ta karbi bakuncin Liverpool a zagaye na uku a FA Cup a watan gobe.

Tsakanin kungiyoyin sun lashe FA Cup guda 22 a tsakaninsu.

Wannan shi ne karon farko da za su fuskanci juna a kofin tun bayan 2-1 da Arsenal ta yi nasara a 2014.

Gunners ta samu nasara a karawa uku baya a gasar, wasan karshe da Liverpool ta ci Arsenal tun a fafatawar karshe a 2001.

Kungiyar da ke buga Championship Sunderland an hada ta wasa da makwabciyarta Newcastle United.

Newcastle za ta ziyarci Stadium of Light a karshen mako na 6 zuwa 7 ga watan Janairun 2024.

Wasu daga fafatawar da za a yi tsakanin masu buga Premier League sun hada da Tottenham da Burnley, Everton da Crystal Palace da na Brentford da Wolves.

Mai rike da kofin Manchester City za ta karbi bakuncin Huddersfield mai buga Championship a Etihad.

Ita kuwa Manchester United za ta je gidan Wigan mai buga Championship..

Leave a comment