Barca da Atletico za su kara a Montjuic karo na uku

Barcelona za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a wasan mako na 15 a LaLiga ranar Lahadi a Montjuic.

Wannan shi ne karo na uku da za su fafata a filin, bayan haduwa a LaLiga da kuma a Super Cup a Estadi Olímpic Lluis Companys.

An gina Estadi Olímpic at Montjuïc a 1929, bayan da Barcelona ta shirya karbar bakuncin duniya a Expo 1929.

Kungiyoyin biyu sun fafata tsakaninsu a shekarar da nufin tallata filing a idon duniya.

Sun kara a Lik a 1928/29, inda Barca ta ci 4-0 a wasan farko, inda Sastre da Walter suka ci mata kwallaye da Samitier da ya zura biyu a raga.

Wasa na biyu kuwa a Montjuïc sun yi shi shekara 67 tsakani da wasan farko.

Sun kara haduwa ranar 25 ga watan Agustan 1996 a wasan farko a Super Cup a Estadi Olímpic, sakamakon filin wasa na Camp Nou yana da matsala.

Atletico, wadda a kakar ta dauki Lik da Cup ta fuskanci Barcelona mai Copa del Rey a Super Cup.

Karawar ita ce ta farko ga sabon koci Sir Bobby Robson da sabon dan wasa Ronaldo Nazário.

Dan kasar Brazil ya ci biyu a wasan da Barcelona ta yi nasara da cin 5-2 a Estadi Olímpic.

A wasa na biyu a gidan Atletico ta ci 3-1, amma dai Barcelona ce ta dauki kofin farko 1996/97.

Haka kuma kociyan Atlético, Diego Simeone yana cikin ‘yan wasa 11 da suka buga wa kungiyar wasan a Agustan 1996.

Atletico mai kwantan wasa tana ta ukun teburin LaLiga da maki 31, iri daya da na Barcelona ta hudu.

Leave a comment