Arsenal ta bayar da tazarar maki hudu a Premier League

Arsenal ta ci gaba da zama ta daya a teburin Premier League, bayan da ta doke Wolverhampton 2-1 ranar Asabara Emirates.

Bukayo Saka ne ya fara ciwa Gunners kwallo, sannan Martin Odegaard ya kara na biyu a wasan mako na 14.

Daga baya ne Wolverhampton ta zare daya ta hannun Matheus Cunha, bayan da aka kusa tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Arsenal tana mataki na daya a kan teburin kakar bana da maki 33.

Sai a ranar Lahadi, mai rike da kofin Manchester City za ta kara da Tottenham.

A kuma ranar ce Liverpool za ta kece raini da Fulham a dai gasar ta Premier League.

Ranar Laraba Arsenal ta kai zagaye na biyu a Champions League, bayan da ta cascara Lens 6-0 a Emirates.

Kungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama za ta je PSV Eindhoven a wasan karshe a rukuni na biyu a gasar zakarun Turai.

Leave a comment