An tsayar da ranar da Messi zai yiwa Inter Miami wasa

Inter Miami za ta kara da tawagar El Salvado a wasan sada zumunta a Estadio Cuscatlan a San Salvador ranar Juma’a 19 ga watan Janairun 2024.

Wasan shi ne na farko da kungiyar da ke buga gasar kwallon kafar Amurka MLS za ta fara yin don shirin tunkarar kakar kasar.

El Salvador, wadda Ruben dela Barrera ke horarwa, mai ‘yan wasa da ke buga MLS ta taka rawar gani a wasan sada zumunta da Curacao.

Haka kuma a shekarar 2024 Inter Miami tana cikin gasar da za ta buga ta Gold Cup da kuma CONCACAF Nations League.

Ana sa ran kyaftin din tawagar Argentina, Lionel Messi zai koma taka leda daga wasa da El Salvado.

Messi tsohon dan wasan Barcelona ya koma Inter Miami daga Paris St Germain.

Leave a comment