Rodrygo ne matashin dan wasa a LaLiga a Satumba

An bayyana dan kwallon Real Madrid, Rodrygo a matsayin matashin dan wasa mai shekara 23 da ba kamarsa a LaLiga a watan Nuwamba.

Cikin watan na Nuwamba, dan wasan mai shekara 22 ya ci kwallo hudu ya bayar da uku aka zura a raga, wanda hakan ya kai Real Madrid mataki na daya a kan teburi.

A wasan da Real ta shararawa Valencia 5-1, Ridrygo ya ci biyu ya bayar da biyu aka zura a raga.

A fafatawa da Cadiz kuwa ya kara cin biyu ya kuma bayar da daya aka zura a raga.

Kawo yanzu Rodrygo, yana cikin kashin bayan ‘yan wasan Carlo Ancelotti, wanda ya buga dukkan wasa 14 a LaLiga.

Haka kuma ya yi karawa biyar a Champions League, wanda jimilla ya ci wa Real Madrid kwallo takwas ya kuma bayar da biyar aka zura a raga.

Tun bayan da Vinicius ya ji rauni a lokacin da yake buga wa Brazil wasan neman shiga gasar kofin duniya a Colombia, Rodrygo ya ci gaba da daukar nauyin Real Madrid tare da Jude Bellingham.

Ranar Asabar 2 ga watan Disamba, Real Madrid za ta karbi bakuncin Granada a wasan mako na 15 a LaLiga.

Real Madrid ce ta daya a kan teburin LaLiga da maki 35, iri daya da na Girona ta biyu, sai Atletico Madrid ta uku mai maki 31, iri daya da na Barcelona ta uku.

Leave a comment