Nagelsmann ya ce Euro 2024 ba zai zo da sauki ba

Kociyan tawagar Germany, Julian Nagelsmann zai halarci jadawalin Euro 2024 da za a yi ranar Asabar 2 ga watan Disamba.

A matsayinta na mai masaukin baki, an saka Jamus a tukunya farko, hakan na nufin ba za ta hadu a da France, England, Belgium, Spain da Portugal a cikin rukuni ba.

Amma watakila za a iya hada ta a cikin rukuni da ko dai Denmark ko Netherlands ko kuma Italy mai rike da kofin.

Nagelsmann tsohon kociyan Bayern Munich, mai shekara 36 ya maye gurbin Hantsi Flick a cikin watan Satumba.

Tuni tawagar ta Jamus ta tsara wasan sada zumunta biyu a watan Maris, kafin a fara gasar daga 14 ga watan Yuni a Munich.

Tawaga 21 da ta kai Euro 2024 sun hada da Germany (mai masaukin baki), Spain, Scotland, France, Netherlands, England, Italy, Turkiye, Albania, Czechia, Belgium, Austria, Hungary, Serbia, Denmark, Slovenia, Romania, Switzerland, Portugal, Slovakia, Croatia.

Yanzu gurbi uku ya rage da za a yi wasannin cike gurbi.

Leave a comment