Everton za ta daukaka kara kan kwashe mata maki 10 a Premier

Ranar Juma’a Everton za ta mika takardun daukaka kara kan kwashe mata maki 10 da mahukuntan Premier League suka yi.

An yiwa Everton hukunci mafi girma a tarihin Premier League, bayan da aka sameta da laifin karya dokar kasuwancin kungiya.

Kungiyar ta amince da ta karya ka’ida, amma ta yi mamaki da irin hukunci mai tsauri da aka dauka a kanta.

Ana sa ran sauraren daukaka karar kafin a kammala kakar Premier League ta bana.

Ba a sanar da kungiyar yadda aka kwashe mata maki 10 daga hukuncin da aka yanke mata ba, amma ta ce ba adalci a ciki.

Hukuncin da aka yiwa Everton ya sa ta koma ta 19 teburi daga ta 14, saura maki biyar ta fice daga cikin ‘yan ukun karshen teburi.

Leave a comment