Super Falcons za ta kara da Cape Verde a Abuja

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria, Super Falcons za ta karbi bakuncin ta Cape Verde ranar Alhamis, domin buga wasan farko a neman shiga gasar kofin nahiyar Afirka.

Tuni dai koci, Justin Madugu ya maye gurbin Asisat Oshoala da Jennifer Echegini, wadanda don radin kansu suka ki amsa goron gayyata.

Wasu ‘yan kwallon da ke jinya sun hada da Halimatu Ayinde da Ifeoma Onumonu  da kuma Michelle Alozie, wadda likitoci za su yi mata aiki.

Madugu ya gayyato Peace Efih, domin maye gurbin Ayinde da Motunrayo Ezekiel, waddat ta maye gurbin Christy Ucheibe.

An kuma kira Chioma Olise don maye gurbin Echegini da kuma Chiamaka Chukwu, wadda ta maye gurbin Oshoalo.

Super Falcons za ta karbi bakuncin wasan farko da Cape Verde a filin wasa na MKO Abiola da ke Abuja, Nigeria ranar Alhamis.

Yayin da za su buga wasa na biyu a Santiago-Estadio Nacional Blue Shark a Praia ranar Talata 5 ga watan Disamba.

‘Yan wasan da Super Falcons ta gayyata:

Masu tsaron raga: Chiamaka Nnadozie (Paris FC); Tochukwu Oluehi (Shualat Alsharqia FC, Saudi Arabia); Christiana Obia (Edo Queens)

Masu tsaron baya: Osinachi Ohale (Pachuca FC, Mexico); Glory Edet (FCF TP Mazembe, DR Congo); Rihanat Kasali (Bayelsa Queens); Oluwatosin Demehin (Stade de Reims, France); Akudo Ogbonna (Remo Stars Ladies); Rofiat Imuran (Stade de Reims, France)

Masu buga tsakiya: Motunrayo Ezekiel (Rivers Angels); Esther Onyenezide (FC Robo Queens); Peace Efih (Sporting Club de Braga, Portugal); Rasheedat Ajibade (Atletico Madrid FC, Spain); Deborah Abiodun (University of Pittsburgh, USA); Toni Payne (Sevilla FC, Spain); Chioma Olise (Edo Queens)

Masu cin kwallaye: Omorinsola Babajide (Coasta Adeje Tenerife Egatesa, Spain); Chiamaka Chukwu (Rivers Angels); Esther Okoronkwo (Coasta Adeje Tenerife Egatesa, Spain); Uchenna Kanu (Racing Louisville, USA); Gift Monday (Coasta Adeje Tenerife Egatesa, Spain)

Leave a comment