An ci wasa 150 da Valverde a Real Madrid

Ranar Laraba Real Madrid ta doke Napoli 4-2 a Champions League, wasan cikin rukuni na uku a Santiago Bernabeu.

Fede Valverde ya buga karawar kuma 150 da aka ci tare da dan kwallon Uruguay, wanda ke kaka ta shida a Real Madrid.

Wasa na 223 da ya buga wa kungiyar Spain kenan, wanda ya ci mata kwallo 19.

Dan wasan ya lashe kofuna da yawa a Real Madrid ciki har da Champions League da Club World Cups biyu da Uefa Super Cups da LaLiga biyu da Copa del Rey da Spanish Super Cups biyu.

Cikin wasa 150 da Real Madrid ta yi nasara tare da Valverde sun hada da 104 a LaLiga da 28 a Champions League da 12a Copa del Rey da biyu a Club World Cup da uku a Spanish Super Cup da kuma daya a Uefa Super Cup.

A bara an ci wasa 38 da Valverde a Real Madrid, wanda ya ci kwallo 12.

Leave a comment