Man United na daf da fita daga Champions League

Galatasaray ta tashi 3-3 da Manchester United a wasan cikin rukunin farko a Champions League ranar Laraba.

Alejandro Garnacho da Bruno Fernandes suka fara ci wa United kwallaye, daga baya Hakim Ziyech ya farkewa Galatasaray daya, haka suka je hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne United ta kara na uku ta hannun Scott McTominay, sai dai kafin a tashi Galatasaray ta farke biyun ta hannun Hakim Ziyech da kuma Kerem Akturkoglu.

Daya wasan na rukunin farko tsakanin Bayern Munich da FC Copenhagen tashi suka yi 0-0 a Jamus.

Da wannan sakamakon Bayern Munich, wadda tuni ta kai zagayen gaba tana da maki 13, sai Copenhagen mai maki biyar iri daya da na Galatasaray da kuma United ta hudun teburi da maki hudu.

Ranar 15 ga watan Disamba za a buga wasannin karshe a rukunin farko, inda Manchester United za ta karbi bakuncin Bayern Munich a Old Trafford.

A dai ranar Galatasaray za ta ziyarci FC Copenhagen a daya wasan na rukunin farko a Champions League.

Man United, wadda take ta shidan teburi, za ta je gidan Newcastle United ranar Asabar 2 ga watan Disamba, domin buga wasan zagaye na 14 a Premier League.

Daga nan United ta karbi bakuncin Chelsea a dai gasar Premier ranar 6 ga watan na Disamba.

Leave a comment