Wasan da Bayern Munich za ta karbi bakuncin FC Copenhagen a Champions League ranar Laraba shi ne na 100 a gasar zakarun Turai.
Wannan shi ne karon farko da Copenhagen za ta ziyarci Allianz Arena.
Kungiyar Jamus mai maki 12 a rukunin farko ta lashe wasa hudu a cikin rukuni har da wanda ta ci Galatasaray 2-1 a cikin watan nan.
Karo na biyar a jere da Bayern ke lashe dukkan wasa hudu a cikin rukuni a Champions League.
Tuni dai Bayern Munich ta kai zagaye na biyu a Champions League karo na 20R.
Real Madrid ce kan gaba a wannan bajintar mai 21, tun daga lokacin da aka sake fasalin gasar a 2003/04.
Haka kuma Bayern ta yi wasa 38 a cikin rukuni ba tare da an doke ta ba, tun wanda PSG ta ci 3-0 ranar 29 ga watan Satumbar 2017, ta yi nasara 35 da canjaras uku.
Kuma kungiyar Jamus ta yi nasara a wasa 17 a jere a karawar cikin rukuni kenan.
Tun bayan da PSG ta yi nasara a kan Bayern da cin 2-1 a Afirilun 2021, tun daga nan ba a kara doke ta ba a gida a wasa 12, wadda ta yi nasara 10 da canajaras biyu.
Shi ne wasan farko da ta yi rashin nasara a Allianz Arena a karawa 21 da cin fafatawa 18 da canjaras biyu.
Tun daga lokacin da Bayern ta tashi 0-0 da Sevilla a cikin Afirilun 2018 – ta ci kwallo 74 a gida.
Wasannin da za a buga ranar Laraba:
- Sevilla da PSV Eindhoven
- Galatasaray da Manchester United
- Arsenal da Lens
- Real Madrid da Napoli
- Real Sociedad da Red Bull Salzburg
- Bayern Munich da FC Kobenhavn
- Sporting Braga da Union Berlin
- Benfica da Inter Milan