Erik ten Hag ya ce a shirye suke da dukkan matsin da za su fuskanta a Galatasaray a Champions League ranar Laraba.
Ranar 3 ga watan Oktoba, United ta yi rashin nasara a hannun Galatasaray da ci 3-2 a Old Trafford.
United za ta buga wasan a Instanbul da cewar ba za ta kai zagaye na biyu ba, da zarar an doke ta a fafatawar.
Wannan shi ne wasan farko bayan shekara 30 da United ta fuskanci kalubale mai dan karen wahala a Galatasaray.
Wasan da United ta doke Everton 3-0 a Premier League a karshen mako ya kara mata kwarin gwiwar tunkakar karawar nan.
A 1993, United ta je Galatasaray da fatan samun sakamakon da zai kai ta fafatawar cikin rukuni, amma hakan bai samu ba.
Bayern Munich ta kai zagaye na biyu da maki 12 a rukunin farko, sai Copenhagen mai maki hudu iri daya da na Galatasaray da kuma United mai uku.
Wasannin da za a buga ranar Laraba:
- Sevilla da PSV Eindhoven
- Galatasaray da Manchester United
- Arsenal da Lens
- Real Madrid da Napoli
- Real Sociedad da Red Bull Salzburg
- Bayern Munich da FC Kobenhavn
- Sporting Braga da Union Berlin
- Benfica da Inter Milan