Ya kamata Arsenal ta dauki Champions League

Kociyan Arsenal, Mikel Arteta ya ce yana kishirwar kofin zakarun Turai, bayan da kungiyar ke daf da kai wa zagaye na biyu a Champions League.

Arsenal za ta karbi bakuncin Lens a wasa na biyar – biyar a cikin rukuni a gasar kofin zakarun Turai a Emirates ranar Laraba.

A wasa na bibiyu a cikin rukuni Lens ce ta yi nasara a kan Arsenal da cin 2-1 cikin watan Oktoba a France.

Gunners na bukatar maki daya, domin ta kai zagaye na ‘yan 16 da za su ci gaba da wasannin Champions League.

Tun bayan da aka bai wa Arteta aikin kociyan Arsenal a 2019, ya kai kungiyar daf da karshe a Europa League a 2021.

Duk da cewa Arteta bai kai kungiyar ga lashe kofin zakarun Turai ba, amma ya kai ta Champions League a karon farko bayan kaka bakwai.

Da zarar Arsenal ta doke kungiyar France ranar Laraba, za ta ja ragamar teburi na biyu zuwa zagayen gaba.

To sai dai Gunners za ta buga wasan ba tare da Fabio Vieira ba, amma watakila ta fara da Kai Havert, wanda ya shiga wasa da Brentford daga baya.

Arsenal, wadda ta taba shekara 20 tana zuwa Champions League a jere, ba ta dauki kofin ba, illa sau daya da ta kai wasan karshe.

Arsenal ce ta daya a rukuni na biyu da maki tara, sai PSV Eindhoven ta biyu mai biyar, iri daya da na Lens da kuma Sevilla mai maki biyu.

Wasannin da za a buga ranar Laraba:

  • Sevilla da PSV Eindhoven        
  • Galatasaray da Manchester United        
  • Arsenal da Lens
  • Real Madrid da Napoli    
  • Real Sociedad  da Red Bull Salzburg       
  • Bayern Munich da FC Kobenhavn  
  • Sporting Braga         da Union Berlin      
  • Benfica da Inter Milan

1 Comment

  • Posted November 29, 2023 12:35 pm 0Likes
    by Safyan Dari Mai-Arsenal Kankara

    Masha-Allahu
    Munajin Dadin Wadannan Labarun naku
    Allah ya Kara Lafiya da Fasaha da Daukaka.

Leave a comment