France ta kai wasan karshe a Fifa under 17

Tawagar Faransa ta kai wasan karshe a Fifa Under 17 da ake yi a Indonesia, bayan da ta doke Mali 2-1 ranar Talata.

Wadda ta lashe kofin matasan a 2001, za ta kece raini da Germany ranar Asabar a birnin Javan a Surakarta.

Germany ta kai wasan karshe ne, bayan da ta yi nasara a kan Argentina a bugun fenariti da ci 4-2, bayan da suka tashi wasan 3-3.

Germany ba ta taba lashe kofin matasa na duniya na ‘yan kasa da shekara 17 ba, amma ta yi nasara a kan France a gasar nahiyar Turai a bugun fenariti, bayan da suka tashi 0-0..

Leave a comment