Bayern ta tsawaita kwantiragin Neuer da Ulreich

Bayern Munich ta tsawaita yarjejeniyar mai tsaron raga Manuel Neuer da Sven Ulreich zuwa karshen kakar Yunin 2025, kamar yadda mai rike da Bundesliga ta sanar.

Neuer ya koma Bayern daga Schalke a 2011 daga nan ya zama kashin bayan kungiyar, wanda yake kyaftin tun daga 2017.

Ya lashe kofi uku karo biyu na Champions League da Bundesliga da German Cup a 2013 da kuma 2020.

Neuer ya lashe kofin Bundesliga 11 a Bayern Munich, wadda ya yiwa wasa 494.

Ana sa ran nan da karshen shekarar nan dan kwallon Jamus zai kai tarihin yawan buga wasanni a Bundesliga, kamar yadda Bastian Schweinsteiger yake da tarihin wasa 500.

Neuer ya yi doguwar jinya, bayan da ya karya kafa a Disambar bara, bayan kammala gasar kofin duniya, wanda ya yi jinyar wata 10.

Ya koma taka leda a cikin watan Oktoba, bai yi wa Jamus wasannin atisaye ba, wadda za ta karbi bakuncin Euro 2024.

Ulreich ya koma Bayern a 2015 daga VfB Stuttgart, wanda ke zaman jiran ko-ta-kwana.

Shi ne Golan Bayern a lokacin da Neuer ke jinya.

Leave a comment