Al Nassr ta kai zagayen gaba a Champions League

Kungiyar da Cristiano Ronaldo ke wasa, Al Nassr ta kai zagayen gaba a Champions League na Asia ranar Litinin.

Kungiyar Saudi Arabia ta tashi 0-0 a gida da Persepoli ta Iran.

Al Nassr ta yi nasarar cin wasa hudu a rukuni na biyar, kuma maki daya take bukata, domin kai wa zagaye na 16.

An yi karo tsakanin Ronaldo da mai tsaron ragar Persepolis, Alireza Beiranvand, inda dan wasan Portugal ya fadi kasa.

Nan da nan ‘yan wasan Al Nassr suka bukaci fenariti, kuma alkalin wasa ya bayar.

Sai dai Ronaldo ya ce ba fenariti bane, inda alkalin wasa ya je VAR ta kuma tabbatar masa, wanda ya soke hukuncin daga baya.

An bai wa dan wasan Al Nassr, Ali Lajami jan kati, bayan da ya yiwa Milad Sarlak keta.

Persepolis, wadda ta lashe gasar zakarun Asia karo biyu ta ci kwallo tun farko aka soke, shi kuwa Ronaldo ya buga wata kwallo mai kyau, amma sai ta bude ta yi waje.

Daga baya an fitar da Ronaldo, mai shekara 38 daga wasan da tuni sun kai zagayen kungiyoyi 16.

Nassr za ta fuskanci Al Hilal ranar Juma’a karawar hamayya a gasar tamaula ta Saudi Arabia.

Leave a comment