Barcelona za ta karbi bakuncin Porto a wasa na biyar-biyar a cikin rukuni a Champions League ranar Talata.
Cikin watan Oktoba, Barcelona ta je Portugal ta ci 1-0, kuma Ferran Tores ne ya ci kwallon.
Porto ce ta daya a cikin rukunin mai maki tara, iri daya da na Barcelona ta biyu.
Barca ta ci karo da koma baya, wadda ta tashi 1-1 da Rayo a La Liga, kafin nan ta yi rashin nasara 1-0 a hannun Shakhtar Donetsk a Champions League.
Barcelona na bukatar cin wasan nan, kai ko canjaras ta yi hakan zai amfane ta maimakon rashin nasara.
Porto, wadda ta lashe kofin zakarun Turai a 1987 da 2004 ta lashe wasa uku a cikin rukuni na takwas.
Koda yake kungiyar ta yi rashin nasara a wasan gida da ta buga da Estoril, hakan ya sa tana ta ukun teburin gasar Portugal.
Barcelona za ta buga wasan ba tare da Gavi ba, wanda ya ji rauni a lokacin da yake buga wa Spain wasa.
Ko kun sani kuwa?
Cikin ‘yan wasan Porto har da Nico González, wanda Barcelona ta sayar da shi ga kungiyar Portugal a cikin watan Yulin bara.
Wannan shi ne wasa na biyar da za su kece raini a Champions League, kuma Barcelona ce ta yi nasara a sauran karawar.
A wasa uku baya ma Porto ba ta samu damar zura kwallo ba a ragar Barcelona.
Barcelona ba ta taba rashin nasara a gida a hannun kungiya daga Portugal ba, illa dai Benfica ta yi wasu canjaras a Spain.
Wasannin da za a buga ranar Talata:
- Lazio da Celtic
- Shakhtar Donetsk da Royal Antwerp
- Manchester City da RB Leipzig
- AC Milan da Borussia Dortmund
- Feyenoord da Atletico Madrid
- FC Barcelona da FC Porto
- Paris Saint-Germain da Newcastle United
- Young Boys da Crvena Zvezda