Werner ba zai buga wa Leipzig Champions League ba

Timo Werner ba zai buga wa RB Leipzig Champions League ba a karawa da Manchester City ranar Talata a Etihad.

Dan kwallon na jinya, wanda bai yi wa kungiyar wasan da ta je Wolfsburg aka doke ta 2-1 a Bundesliga ranar Asabar ba.

Watakila Benjamin Sesko yam aye gurbin Werner.

Shima bai yi karawar ta Wolfsburg ba, saboda ciwon wuya, amma ya yi atisaye ranar Litinin.

Saboda haka ana sa ran zai buga wasa na biyar-biyar a cikin rukuni a Etihad ranar Talata.

A wasa na bibiyu a cikin rukuni, Manchester City ta je ta doke Leipzig 3-1 a Jamus a gasar ta zakarun Turai ta bana.

Leipzig da City sun kai zagaye na biyu a Champions League, duk da saura wasa bibiyu a kammala karawar rukuni.

Leipzig na bukatar cin Manchester City a Etihad, idan har tana son yin ta daya a rukunin.

Leave a comment