Watakila Liverpool ta dauki Leroy Sane a Janairu

Watakila Liverpool ta dauki dan kwallon Bayern Munich, Leroy Sane a watan Janairu.

Ana ta rade-radi kan makomar dan kwallon tawagar Jamus a Munich, bayan da kwantiraginsa zai kare a karshen 2025.

Ana cewa Manchester City na fatan sake daukar dan wasan mai shekara 27, Manchester United ma na son yin zawarci.

Sane kashin bayan Munich ne, wanda ya ci kwallo takwas ya bayar da 12 aka zura a raga.

Dan kwallon ya koma Jamus da taka leda daga Manchester City a kakar 2020, ya buga wa Munich wasa sama da 150 da cin kwallo 47 ya bayar da 44 aka zura a raga.

Liverpool na neman wanda zai maye gurbin Mohamed Salah, idan ya je gasar kofin Afirka da za a yi a Ivory Coast daga cikin Janairu zuwaFabrairun 2024

Leave a comment