An bai wa Ramos jan kati na 29 ranar Lahadi

An bai wa Sergio Ramos jan kati kuma na 29 a tarihin taka ledarsa a wasan da Real Sociedad ta ci Sevilla 2-1.

Ranar Lahadi Sevilla ta ziayrci gidan Real Sociedad wasan mako na 14 a gasar ta Spain.

An kori tsohon mai tsaron bayan Spain da Real Madrid saura minti biyu a tashi wasan, bayan keta da ya yiwa Brais Mendez.

A ranar Lahadi dan wasan mai shekara 37 ya ci gaba da zama kan gaba a yawan karbar jan kati a La Liga.

Dan wasan Sevilla, Jesus Navas, mai shekara 38 ya karbi jan kati a karon farko a tarihin tamaularsa, bayan korafi kan korar Ramos.

Bayan Ramos mai jan kati 29a La Liga, masu biye da shi sun hada da Rafael Marquez mai 21 da Felipe Melo 20.

Jan katin farko da aka bai wa Ramos kenan tun bayan da ya koma kungiyarsa, wadda tun yana matashi kan fara kakar bana.

Kawo yanzu Sevilla ta yi wasa bakwai ba tare da nasara ba, wadda ta yi kasa zuwa ta 15, ita kuwa Sociedad tana ta biyar.

Leave a comment