Ko Girona za ta koma ta daya a teburin La Liga?

Ranar Litinin Girona za ta karbi bakuncin Athletic Bilbao a karashen wasan mako na 14 a gasar La Liga.

Girona ta doke Bilbao gida da waje a kakar bara, wadda ta ci 2-1 a wasan farko ranar Juma’a 4 ga watan Mayun 2022.

Karawa ta biyu kuwa a gidan Bilbao doke ta 3-2 Girona ta yi ranar Lahadi 26 ga watan Fabrairun 2023.

Kawo yanzu Real Madrid ta dare matakin farko da maki 36 da tazarar maki daya kenan tsakaninta da Girona.

Ranar Asabar Real ta je ta ci Cadiz 3-0, inda Rodrygo ya ci biyu, sannan Jude Bellingham ya kara na uku na 11 jimilla a La Liga ta bana.

Idan Girona ta ci wasan ranar Litinin za ta koma matakinta na farko a kan teburin babbar gasar tamaula ta Spain.

Ita dai Bilbao tana ta shidan teburi mai maki 24, kuma Atletico Madrid ce ta uku da maki 31, iri daya da na Barcelona ta hudu.

Leave a comment