Ko Manchester United za ta doke Everton?

Everton za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan mako na 13 a Premier League da za su kara a Goodison Park ranar Lahadi.

United mai maki 21 tana ta takwas a kan teburin Premier League, ita kuwa Everton tana ta biyun karshe mai maki hudu.

Everton ta koma wannan matakin bayan da aka kwashe mata maki 10, bayan da aka sameta da laifin karya dokar Premier League kan kasuwanci.

Wasa biyu kacal Everton ta yi nasara daga 19 da ta fuskanci United a Premier League.

Wasannin sune a Goodison Park, inda ta ci 4-0 a cikin Afiilun 2019 da 1-0 a Afirilun 2022.

Watakila Everton ta yi rashin nasara a hannun United a Premier League karo na 40.

Daga cikin kungiyoyin da United ta ci wasa da yawa sun hada har da Tottenham karo 39.

A bara gida da waje United ta doke Everton, watakila ta yi nasara karo na biyu a Goodison Park a jere, wadda rabon da ta yi hakan tun bayan wasa uku daga 2005 zuwa 2007.

Leave a comment