Juventus za ta karbi bakuncin Inter Milan a wasan mako na 13 a gasar Serie A ranar Lahadi.
A wasan na hamayya, Inter ce ta daya a kan teburi da maki 31, ita kuwa Juventus tana ta biyu mai maki 29.
Kungiyoyin biyu sun kara sau hudu a bara, inda suka fara a Serie A ranar 6 ga watan Nuwambar 2022, Juventus ce ta ci 2-1.
Ranar 19 ga watan Mayun 2023 suka kara a wasa na biyu, Juventus ta je ta doke Inter 1-0 a dai Serie A.
A Copa Italia kuwa da suka yi a wasan farko ranar 4 ga watan Mayun 2023, sun tashi 1-1.
Karawa ta biyu kuwa ranar 26 ga watan Afirilun 2023, Inter ce ta yi nasara da cin 1-0 a dai Copa Italia.
Dan wasan Inter, Lautaro Martinez, shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye mai 12 a raga.
Wasannin mako na 13 da za a buga ranar Lahadi
- Cagliari da AC Monza
- Frosinone da Genoa
- Empoli da Sassuolo
- AS Roma da Udinese
- Juventus da Inter Milan