Lakers ta yi nasarar doke Cavaliers a NBA

Los Angeles Lakers ta doke Cavaliers da cin 121-115 a gasar kwallon Amurka ranar Asabar a Cleveland.

Dan wasan Los Angeles, Anthony Davis ya ci maki 32 a zagaye na biyu.

Cav ta hada maki 40 a zangon farko, wadda ta ja ragama da cin 71-70.

Sauran minti 3:48 a tashi daga fafatawar Lakers ta saka kwazon da ta hada maki 111-103.

Donovan Mitchell, ya buga karawar, wanda ya yi jinyar da bai yi wasa hudu baya ba, ya hada maki 22 da kuma Jarrett Allen mai 21.

A birnin Oklahoma kuwa, Philadelphia ce ta doke Thunderda ci 127-123.

Fitatcen dan wasa Joel Embiid ya hada maki 35 a karawar.

Leave a comment