‘Yan Real Madrid da za su fafata da Cadiz a La Liga

Cadiz za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan mako na 14 a gasar La Liga ranar Lahadi.

Cadiz, mai maki 10 tana ta 16 daga kasan teburin La Liga, Real kuwa tana ta biyu da makinta 32.

Kungiyoyin biyu sun kara a bara, inda Real ta ci Cadiz 2-1 ranar Alhamis 10 ga watan Nuwambar 2022.

Yayin da Cadiz ta yi rashin nasara a wasa na biyu a La Liga da ci 2-0 ranar Asabar 15 ga watan Afirilun 2023.

Girona ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 34, wadda za ta karbi bakuncin Athletic Bilbao ranar Lahadi.

Athletico Madrid ce ta ukun teburi da kuma Barcelona ta hudu, wadda ta tashi 1-1 a gidan Rayo Vallecano ranar Asabar.

Tuni dai Real Madrid ta sanar da ‘yan wasan da ta je da su Cadiz, domin buga wasan na mako 14 a Nuevo Mirandilla.

‘Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Lunin, Diego Piñeiro da kuma Fran.

Masu tsaron baya: Carvajal, Alaba, Nacho, Lucas V., Fran García, Rüdiger da kuma Mendy.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Valverde, Ceballos, Mario Martín da kuma Nico Paz.

Masu cin kwallaye: Rodrygo, Joselu, Brahim da kuma Gonzalo.

Wasannin da za a buga ranar Lahadi

  • Villarreal da Osasuna      
  • Real Sociedad da Sevilla
  • Cadiz da Real Madrid
  • Real Betis da Las Palmas
  • Girona da Athletic de Bilbao

Leave a comment