Ƙungiyar Barcelona ta yi ban kwana da Copa del Rey, duk da cin Atletico Madrid 3-0 a wasa na biyu da suka kara a gasar ranar Talata.
Karawar daf da karshe suka buga a Camp Nou, bayan da wasan farko Atletico ta ci 4-0 ranar 12 ga watan Fabrairu, kuma karo na uku da suka fafata a kakar nan.
Barcelona ta ci Atletico 3-1 a gasar La Liga cikin watan Oktoban 2025, za kuma su kara fuskanta juna a cikin watan Afirilu a LaLiga a gidan Atletico.
A wasan da Barcelona ta karɓi bakunci ranar Talata ta ci ƙwallayen ta hannun Marc Bernal da ya zura biyu a raga da kuma Raphinha.
A ranar Laraba za a buga ɗaya wasan daf da karshe tsakanin Real Sociedad da Athletic Club, kuma duk wadda ta yi nasara za ta fuskanci Atletico Madrid a karawar karshe. Barcelona ce mai kofin bara.
Barcelona me fama da ƴan wasa da ke jinya ta rasa Andreas Christensen da kuma Eric Garcia, shi sakamakon hukuncin dakatarwa.
Pedri ya murmure, amma Frenkie de Jong da saura da kuma Robert Lewandowski bai murmure ba.
Itama Atletico na fama da ƴan wasan da ke jinya da ya haɗa da Pablo Barrios da kuma Johnny Cardoso.
Barcelona za ta je Athletico Bilbao ranar 7 ga watan Maris a gasar LaLiga, ita kuwa Atletico za ta karɓi bakuncin Sociedad a dai ranar.
